Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rasha Putin Ya Soke Kai Ziyara Faransa


Shugaban Rasha Vladimir Putin a majalisar kasarsa
Shugaban Rasha Vladimir Putin a majalisar kasarsa

Shugaba Vladimir Putin ya soke shirin kai ziyara Faransa, bayan da shugaba Francoise Hollande ya jaddada cewa tilas ganawarsu ta maida hankali kan rikicin da ake yi a Syria.

Ana sa ran Putin zai yi balaguro zuwa Paris ranar 19 ga watan nan, ziyarar da zata hada bikin bude wata sabuwar Chocin masu ra’ayin rikau

Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya fada yau Talata cewa a shirye shugaba Putin yake ya gana da shugaba Hollande a duk lokacin da shugaban na Faransa ke da sarari, yayinda shi kuma Mr. Hollande ya fadi cewa har yanzu a shirye ya ke don ganawa muddin shawarwarin zasu kai ga "karfafa zaman lafiya".

Ranar Litinin ministan harkokin wajen Faransa Jean - Marc Ayrault ya ce Rasha na iya fuskantar zargin aikata laifukan yaki saboda hare-haren da take kaiwa a birnini Aleppo dake arewacin Siriyya.

Mr. Jean-Marc ya kuma ce faransa zata tuntubi mahukunta daga kotun duniya don ganin yadda za a kaddamar da bincike.

Duk da dai Rasha ta sha karyata batun kai hari kan farar hula a Siriyya, tana mai cewa ita fa kungiyoyin ‘yan ta’adda ta auna don goyawa shugaba Bashar al-Assad baya

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG