Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayraut ya sahidawa wata radiyon Faransa a jiya Litinin cewa sakin bama bamai laifi ne na yaki.
Yace ciki kuma har da wadanda suka yi hadin guiwa wurin tabka wannan ta’asa dake faruwa a yankin Aleppo har da kuma shugabannin Rasha.
Ayrault yace Faransa zata nemi shawarar masu shigar da kara na babban kotun kasa da kasa, ta ga yanda zata gudanar da bincike.
Rasha dai tana ci gaba da musunta cewa ta kai hari a kan fararen hulan a Syria, tace kan yan ta’adda kawai take aunawa a hare-haren nata.
Haka kuma Ministan harkokin wajen Faransa yace mai yiyuwa ne shugaban Francios Hollande ya ki saduwa da shugaban Rasha Vladmir Putin, wanda zai kai ziyara a kasar ta Farnsa a mako mai zuwa.
Yace in kuwa shugaban Hollande ya sadu da Putin ba zai zama saduwa ta anashuwa ba, sai dai zai zama tattauanwa ta fadawa juna gaskiya.