Wani dan majalisar jiha mai goyon bayan shugaba Donald Trump wanda ya dauki bidiyon kansa ya na shiga ginin majalisar dokokin Amurka ya yi murabus kuma an sanar da karin kamen masu tarzoma a jiya Asabar a zaman wani bangaren binciken da ake yi akan harin da aka kai ranar Larabar da ta gabata a ginin majalisar dokokin Amurka.
Derrick Evans, dan majalisar wakilai a jihar West Virginia daga jam’iyyar Republican, ya sanar da yin murabus din ne a jiya Asabar a wata wasika da ya turawa gwamnan jihar West Virginia Jim Justice.
Ana tuhumar Evans ne akan shiga wurarren da sai da izini ake shiga a ginin majalisar da kuma saba doka da oda. Idan aka same shi da laifi, zai fuskanci hukuncin daurin shekara 1 da rabi a gidan yarin gwamnatin tarayya.
Evans ya yada bidiyon kansa a shafin Facebook a lokacin da ya afka cikin ginin tare da wasu masu tarzomar, akwai lokacin da aka ji ya na cewa “mun shiga ciki.” A wani bidiyon da ya sanya a Facebook kafin lokacin kuma, wanda daga baya aka cire, Evans ya yi gargadin cewa masu tarzomar zasu shiga ginin majalisar.