Da alama manufar taron jam'iyyar PDP da shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta a Sokoto ta wuce ta karbar Attahiru Bafarawa da magoya bayansa kadai domin shugaban ya yi kokarin bayyanawa duniya cewa jam'iyyar tana nan daram da kwarjininta duk da rigingimun da ta sha fama da su tare da ficewar wasu gwamnoni. Shugaban ya ce suna son su yi anfani da jihar Sokoto a zaman misali cewa har yanzu jam'iyyar PDP ita ce mafi yawa da karfi a duk fadin Najeriya.
A cigaba da jawabinsa a Sokoto shugaban kasa ya kaucewa fitowa fili ya fada ko zai sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa abun da kowa ke jira ya ji. Sai dai ya ce har yanzu jam'iyyarsa bata tsayar da kowa ba tsayawa zabe. Babu wani dan takara a jam'yyar yanzu.
To sai dai 'yan kasuwar kara da ta kone kwanan nan Allah Ya yi masu gydar dogo domin yayin da shugaban ya ziyarci kasuwar ya basu taimakon nera miliyan 250 kana ya yi masu alkawarin taimako daga gwamnatin tarayya.
To sai dai jam'iyyar adawa ta APC ta mayarda martani kan ziyarar. Ta ce siyasa ce kawai. Shugaban kungiyar matasan 'yan kasuwa ta jihar Sokoto Alhaji Kabiru Hali ya ce an yi gobara a kasuwanni daban daban a cikin Sokoto duk da an sanarda shugaban kasar bai taba zuwa Sokoto ya jajantawa wadan da suka yi asara ko kuma ya aiko da taimako ba.
Duk da cewar APC bata damu da zuwan shugaban ba amma ta fusata da Sanato Muhammed Ahmad Maccido da ya ki bin sawun takwarorinsa wajen komawa APC. Jam'iyyar ta ce ta la'anci sanatan kuma basa tare da shi. Amma Bafarawa ya jinjinawa sanatan da ire-irensa da suka tsaya cikin PDP.