Gwamnatin jihar Taraba ta sha damarar dakile ayukan ‘yan bata gari da aka kora daga wasu jihohi makwabta da ke assasa tashe-tashen hankula a wasu sassa na jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Taraba Ijiniya Haruna Manu ya bayyana haka lokacin da ya kaiwa ‘yan gudun hijra da harin ranar Lahadin makon jiya ya rutsa da su a sansanonin Kungana, Garbabi da Mayo-salbe doki na kayan abinci, maganguna, kayan masarufi da taburmai.
Wata ‘yar gudun hijira malama Saferiya Christopher mai ‘ya’ya uku, karami daga cikin su dan watanni shida da haihuwa ta shaidawa wakilinmu Sanusi Adamu cewa da ta rasa ‘ya’yanta ga yunwa cututtuka ba domin dokin gaggawa da gwamnati ta kai masu cikin lokaci ba. Shima Ishaya Samaila ya ce yara kanana sun iso sansanin cikin hali na galabaita da fama da cututtuka sakamakon tafiyar kilomitoci da dama kan tsaunuka kamin su isa sansanonin.
A halin yanzu ‘yan gudun hijira sama da dubu shida ke tsugune a sansanoni uku yayin da rahotanni da ba a tantance ba ke nuni da dubbai da suka famtsama akan tsaunukan Gembu, Sarti da Kurmi domin gudun kada maharan su far masu ne ke fuskantar matsalar yunwa.
Ga karin bayani.