Jihar Kaduna zata kashe kashin 64, na kasafin kudinta akan manyan aiyuka more rayuwa ga ‘yan jihar, yayin da bangaren yau da kullum ya samu kashi 36 cikin 100, na kasafin kudin shekarar2016.
To ko a ina Gwamnatin jihar Kaduna zata samu kudaden da zata yi amfani dasu a kasafin kudin shekarar 2016, tunda an wayi gari farashin mai yayo kasa a kasuwar duniya.
Gwamna El- Rufai, ya ce ya zama wajibi jama’a su biya haraji, ko na gida ko kuma na masana’antu, domin a cewarsa da wannan kudin ne za’a gyara jihar.
Sai dai a dai dai lokaci da Gwamnan ke gabatar da wannan kasafi wasu aluma daga yankin Zaria, Zanga Zangar nuna damuwa game da shirin Gwamnati jihar Kaduna na rushe wasu gidaje da suka shafesu.
Masu zanga zangar da suka hada da Mata, Matasa yara da masu gida sun yo cincirindo ne zuwa cibiyar ‘yan jaridu ta jihar Kaduna, inda suka yima ‘yan jaridu Karin haske game da abinda ke damunsu.
Mai Magana da yawun Gwamnan jihar Kaduna Mr. Samuel Aruwan, ya ce dukkanin masu wannan korafi basu da takardan mallakar filayen, kuma Gwamnatin batana wannan bane domin cin fuskar su bane.