A ranar Litinin, jaridun Najeriya sun ruwaito bayanin mukaddashin daraktan kula da harkokin sadarwa a babban bankin Najeriya, Mr Isaac Okorafor cewa, kulla yarjejeniyar ba yana nufin mayar da Najeriya dandalin tara kayyakin kamfanonin China ba ne.
Saboda haka, manufar gwamnati ta hana shigo da wasu kayayyaki daga ketare domin habaka masana’antun cikin gida tana nan daram.
Malam Attahiru Magaji Gwarzo da ke zaman babban Jami’i a cibiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da ayyukan noma ta jihar Kano ya ce akwai alfanu a kunshin yarjejeniyar, to amma tilas sai an yi hakuri.
Ya kara da cewa , abin na da amfani ga tattalin arziki musamman na Najeriya wanda ya dogara da kayayyakin da ake shigowa da su, hakan zai taimaka wajen rage dogaro da ake yi kan dalar Amurka, kuma zai ragewa 'yan kasuwa wahalhalun samun kudi.
Kayyaki guda 41 da gwamnatin Najeriya ta haramtawa shiga da su cikin kasar kuma masu hada-hadarsu ba za su fa’idantu da wannan tsari na musayar kudi da China ba, sun hada da shinkafa da kwanon rufi da tumatirin gwangwani, da tufafi, da dai sauransu.
Sai dai Alhaji Aminu Dangana, Manajan Daraktan kamfanin harkokin hannayen jari na gidauniya na cewa ko da yaushe gwamnati awon gaban ta take yi,kamata ya yi a ce ta fahimtar da 'yan kasuwa abin da take yi kafin ta aiwatar da hakan.
Facebook Forum