Mai fafutukar ‘yancin dan adam din nan da ta taimaka wajen fara yakin a bar mata su tuka mota a Saudiyya, ta ce, tana samun sakonnin da ke barazana ga rayuwarta, yayin da aka tunkarin lokacin dage dokar.
A shekarar 2011, an taba rufe Manal al-Sharif, bayan da ta saka wani hoton bidiyonta tana tuki a kasar ta Saudiyya, kasar da ita ce kadai ta haramtawa mata tuki a Duniya.
Al-sharif, wacce yanzu haka take zaune a kasar Australia, ta fadawa kafafen yada labaran cikin gida a jiya Litinin cewa, tana da shirin komawa kasarta, ta kuma tuka mota ta zagaya kasar, idan an dage dokar a ranar 24 ga watan Yuni.
Amma kuma ta yanke shawarar cewa za ta zauna a Sydney,babban birnin Australia, bayan da aka tsare wasu fitattun masu fafutukar ‘yancin dan adam su bakwai a karshen makon da ya gabata a Saudiyyan.
A cewar Al-Sharif, an kira dumbin masu fafutuka a wayar talho, inda aka gargadesu da kada su yi tsokaci kan dokar da ta yi magana kan dage tsari haramta tukin mota ga mata a kasar ta Saudiyya, tana mai cewa mutane bakwan da aka tsare, suna cikin wadanda ke ci gaba da magana kan lamarin.
Facebook Forum