A Thailand dubban 'Yansandan kasar ne suke sintiri kan titunan birnin Bangkok, yayinda masu zanga zanga suke shirin yin maci domin tilastawa sojojim kasar su gudanar zabe.
Duk da haramta ko wani irin gangami na siyasa, masu zanga zanga sun hallara domin tunawa da cikar shekaru 4 bayan juyin mulkin da sojoji suka yiwa gwamnatin Yingluck Shinawatra ranar 22 ga watan Mayu shekara ta 2014.
Firayim Minista Prayut Chan-O-Cha, wanda shine babban hafsan hafsoshin kasar lokcinda suka kifar da gwamnatin, yace za'a gudanar da zabecikin watan Febwairun badi, sai dai masu zanga zangar sun ce basu da tabbas kan jadawalin zaben da sojojin suka shirya, saboda haka suna so a yi zaben cikin watan Nuwamba. Sojojin sun sha jinkirta zaben, wadda da farko suka ce za'a yi cikin shekara ta
Facebook Forum