Bincike ya nuna cewa kimanin kashi saba’in bisa dari na magungunan zazzabin cizon sauro da ake sayarwa a Najeriya jabu ne abinda yasa masu fama da cutar basu samun cikakken maganin da suke butaka a kan lokaci.
Bisa ga cewar kwararru, shan irin wannan maganin yana da illar gaske domin banda hana cutar kin jin magani, yana kuma sawa mai fama da cutar ya rika kamuwa da ita a kai a kai wadansu lokuta ya kai ga mutuwa. Ta dalilin haka kwararru suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da kudi da za a gudanar da bincike yadda kuma jami’an aikin jinya zasu rika kara samun zurfin ilimi game da jinyar zazzabin cizon sauro.
Kwararru suna kuma so cibiyar da take sa ido kan ingancin magunguna ta dauki kwararan matakan yaki da jabun magunguna musamman maganin zazzabin cizon sauro.