Zazzabin cizon sauro yana daya daga cikin cututakan da suka fi kashe mutane a duniya. Hukumar Lafiya tayi kiyasin cewa, kimanin mutane miliyan dubu dari uku da talatin suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar a shekara.
Hukumar lafiya ta bayyana cewa, ko da yake ana iya shawo kan zazzabin cizon sauro, yana ci gaba da kama sama da mutane miliyan dari biyu yayinda yake kuma kashe kimanin mutane dubu dari shida da sittin kowacce shekara.
Duk da haka hukumar ta bayyana cewa, ana iya cimma burin muradun karni na shawo kan cutar kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar. Hukumar lafiyar tace kawo yanzu kasashe hamsin sun yi nisa a yunkurin cimma burin shawo kan cutar da kimanin kashi 75% a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.
Hukumar Lafiya ta bayyana cewa, shirin yaki da zazzabin cizon saura na kasa da kasa ya taimaka wajen ceton rayukan mutane miliyan daya da dubu dari da kuma jinyar kimanin mutane miliyan dari biyu da saba’in da hudu tsakanin shekara ta dubu biyu da daya zuwa dubu biyu da goma. Bisa ga cewar hukumar ana samun kashi 80% na zazzabin cizon sauro ne a kasashen da cutar tayi muni, kashi 40% daga ciki kuma daga kasashe uku da aka fi fama da zazzabin cizon sauro da suka hada da Najeriya, da Congo da kuma India.
Babbar kalubalar da ake fuskanta a halin yanzu a yaki da cutar shine, kin jin magani da kwayar cutar zazzabin cizon sauro take yi.