Jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da ke arewacin Najeriya, sun fara bin sahun mutanen da ke zuwa yin allurar riga-kafin cutar korona.
Daga cikin jaruman akwai Aminu Shariff Momo da Rashida Mai Sa’a, wadanda suka wallafa hotunan lokacin da ake musu allurar a shafukansu na Instagram.
“Na karbi allurata a yau, tana da inganci kuma ba ta tattare da wani hadari.” In ji Momo.
"A yau, na karbi allurar Oxford AstraZeneca. ku je a yi muku ta ku yanzu" In ji Ali Nuhu.
Ita kuwa jaruma Rashida Mai Sa’a cewa ta yi, “mun karba, mu ma a kula da mu,” inda bayan da aka yi mata allurar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da tsaro a kasar.
“Ya kamata a zuba mana matakan (jami'an) tsaro su kula da rayuwarmu, tun da an mana allurar korona, a saka mana matakan tsaro daga masu garkuwa da mutane, kowa ya yi bacci a gidansa.” Rashida ta ce.
A ‘yan makonnin da suka gabata aka fara aikin yin allurar nau’in AstraZeneca a wasu sassan Najeriya yayin da jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar, ta fara yi wa al’umarta a makon da ya gabata.
A baya-bayan nan hukumomin Kano suka yi korafin cewa jama’a ba sa fita domin karbar allurar a daidai lokacin da was uke nuna shakku kan riga-kafin.
Hakan na faruwa ne yayin da allurar AstraZeneca take fuskantar suka a sassan duniya kan cewa tana haifar da daskarewar jini.
Ko da yake, hukumomin lafiya na duniya sun sahale a ci gaba da yin amfani da ita suna masu cewa alfanunta ya fi illar da take haifarwa.