Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaridar Washington Post Ta Fasa Kwai Akan Surukin Donald Trump


 Shugaba Donald Trump da Jared Kushner
Shugaba Donald Trump da Jared Kushner

Wannan asirin ya tonu ne a lokacin da jami'an Amurka suka karanta wasu bayanan Rasha da aka cafke

Jaridar Washington Post ta fasa kwan cewa Jared Kushner, surukin shugaba Donald Trump kuma babban mashawarcinsa, ya nemi alfarma daga jakadan Rasha dake Washington, cewa a bude wa gwamnatin ta Trump wata kebantacciyar hanyarwa sadarwa ta kai tsaye tsakanin mukarabban Trump masu shirya musayar ragamar mulki (tsakaninsu da gwamnatin da suka gada) da kuma gwamnatin ta Rasha, hanyar kai tsaye ba sai an bi ta wasu hanyoyi na ma’aikatu ko jami’an diplomasiyar Amurka ba.

Jaridar tace mutanen Trump din sunyi hakan ne don rufe asirin duk tattaunawar da suka gudanar yayinda ake shirye-shiryen hawansu kan karagar mulki.

Jaridar tace jakadan na Rasha, Sergei Kislyak ya kai maganar zuwa wajen manyansa dake birnin Moscow, inda ya gaya musu cewa Kushner ya nemi wannan alfarmar ne a ganawar da suka yi da juna a gidan Trump din dake New York a farkon watan Disamba.

Kafofin dake bada bayanin sunce asirin ya tono ne a lokacinda jami’an Amurka suka karanta wasu bayanan Rasha da aka cafke.

Yanzu haka dai an bada rahoton cewa Hukumar Binciken Manyan Laifukka ta FBI ta soma gudanarda bincike akan shi Kushner din.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG