Janaral Muhammed Buharia a taron majalisar zartaswar jam'iyyar APC ya nanata allawadai da yadda tsarin daukan ma'aikatan hukumar shige da fici ya yi sanadiyar mutuwar wasu dake neman aikin. Shi ma Aminu Bello Masari mataimakin jam'iyyar na kasa yace abun da ya tada hankali an ce guraben aikin dubu hudu da dari biyar ne. Cikin wadannan an ce mutane 240 ne kawai za'a dauka. Amma kuma mutane fiye da dubu dari bakwai suka sai takardar daukan aiki kan nera dubu dubu. A halin da ake ciki a sa talaka ya kashe nera dubu ya sayi abun da babu tamkar rashin gaskiya ne.
Bello Masari ya kara da cewa 'yan Najeriya su sani cewa babu alheri a gwamnatin PDP kuma babu abun da zata tsinatawa kasar. Gwamnatin bata da fatan alheri ga mutanen Najeriya. Yace babbar matsifa da take tasarwa kasar ita ce rashin aikin yi musamman ga matasa. Amma APC akwai abubuwa da yawa da ta shirya zata yi da zarar ta samu kama madafin ikon kasar.
Gwamnan Jihar Imo Rogas Okorocha yace basu ji dadi ba kan yaran da suka rasu wurin neman aiki. Gwamnati ta san ma'aikata dubu hudu take nema menene na sayarda takardu har dubu dari bakwai da 'yan kai a kan nera dubu dubu?
Taron ya zo ne a lokacin da gwamnatin PDP ta zargi 'yan adawa da yiwa gwamnatin zagon kasa ta hanyar haddasa rikici domin hana shugaba Jonathan yin sakat sabili da wai domin shugaban ya fito ne daga karamar kabila
Ga karin bayani.