Dan takarar shugabancin Najeriya, a karkashin tutar jam’iyyar APC janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya gargadi yan takarar gwamna a jam'iyar sa dasu tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifin barnata kudaden jama'a to lalle zaije gidan yari.
Janar Buhari dai yayi wannan gargadin ne a jihar Gombe, a wajen gangamin yakin neman zabe da aka gudanar a jiya Talata.
Inda Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, yayi kira ga gwamnatocin jam’iyyar APC, wanda yace, “Zamuja layi sannan muyi gaba, amma daga wannan duk wanda aka bawa amanar jama’a da kudin baitulmali idan yaci yasan abinda yaci, kuma yasan inda zai karkare. Ranar da zamu samu daga hana zaluncin sata, zamuyi amfani da ita domin gina makarantu, asa kayan aiki, a samu malamai, saboda babu abinda za’a bawa al’umma fiye da ilimi, idan aka bawa al’umma ilimi zasu kula da kansu.”
Idan aka lura dai da zafafa yakin neman zabe da jam’iyyar PDP da APC ke karade jihohin Najeriya domin neman jama’a su zabesu a manyan zabubbukan dake tafe cikin wannan watan.