WASHINGTON, DC —
Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, wato, FIFA, Yarima Ali bin al-Hussein, yace Amurka, na cikin kasashen da zasu mara masa baya don takarar neman shugabancin hukumar FIFA.
Da asalin kasar Jordan, al- Hussein, ya sami goyon bayan kasar sa, da kuma kasashe kamar su Belarus, Malta, England da kasar Georgia.
Hukumar kwallon kafa ta Afirka, da ta kudancin Amurka, sun amince da Sepp Blatter ya sake tsayawa .
Yerima al-Hussein, yace a can baya Sepp Blatter, yayi alkawarin cewa ba zai sake tsayawa takarar neman shugabantar hukumar ta FIFA ba.
Ya kara da cewa a kashin gaskiya ya kyautu Sepp Blatter, ya hakura da shugabancin hukumar FIFA, saboda ya baiwa wasu damar shugabatar hukumar domin taka tasu rawar.