Masu kada kuri’a a kasar Burma, sun kada a yau Lahadi, a zaben Majalisar Dokokin da ake ganin shi ne zakaran gwajin tafin sauye-sauyen dimokaradiyyar kasar.
An yi takarar kujeru 45 na Majalisar mai kujeru 664, a zaben zagaye na biyu, na farko tun bayan da sabuwar gwamnatin, shigin ta dimokaradiyya ta karbi ragamar mulki a watan Maris na bara.
Babbar jagoriyar ‘yan adawa Aung San Suu Kyi, wadda ke shugabantar Jam’iyyar Dimokaradiyya ta Kasa (NLD a takaice), ta tsaya takara a karo na farko tun bayan 1990, lokacin da jam’iyyarta ta yi gagarumar nasara a babban zabe. A wancan lokacin, shugabannin mulkin soja sun ki mika ragamar mulki, sai su ka mata wani irin dauri, a akasarin tsawon shekaru 20 da su ka biyo baya.
Jam’iyyar ta NLD ta yi zargi a yau Lahadi cewa an rufe wasu daga cikin takardun zaben da ruwan kendir, ta yadda daga bisani ana iya kankarewa a canza sakamakon kuri’ar. Bangaren na adawa ya kuma yi zargin an yi barazana wa masu kada kuri’a. Aung San Suu Kyi dai ta ce ba ta sa ran zaben na Burma zai yi inganci, to amman ta ce duk ko da haka wani cigaba ne.
Wani babban zaben da aka yi a 2010 da masu samun goyon bayan sojoji su ka ci, ya gamu da koke-koken magudi da rashin shigar NLD, wadda ta kaurace wa zaben saboda an hana jagoriyar jam’iyyar tsayawa takara.