Firai Ministan kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya na kasar China, inda zai gana da manyan jami’an gwamnatin kasar domin su kulla huldar kut da kut a fannin cinikayya da siyasa.
A ziyarar aikin da wani firai ministan kasar Turkiyya ya kai China cikin shekaru 27, Mr.Erdogan ya samu tarbon karramawa da shimfidar jan darduma da kade-kaden taken kasashen biyu, da kuma jerin jami’an tsaron ban girma a Beijing. A yau Litinin zai gana da shugaba Hu Jintao da Pirimiya Wen Jiabao da kuma mataimakin shugaban kasa Xi Jinping.
Ministan makamashin kasar Turkiyya, Taner Yildiz ya ce a yayin ziyarar da Mr.Erdogan ya ke yi a kasar China, gwamnatin kasar Turkiyya za ta yanke shawara ko za a gayyaci Chinar ta ginawa Turkiyya masana’antar makamashin nukiliya a gabar tekun Bahar Aswad. Bangarorin biyu za su daddale batun gina masana’antar a yayin wannan ziyara.
Kafin Mr.Erdogan ya isa birnin Beijing tare da wata tawagar ‘yan kasuwa 300, sai da ya fara yada zango a jiya Lahadi a yankin Xinjiang a can gabashin kasar China mai nisa. Yankin na Xinjiang mai fama da tashin hankali, mazauni ne ga ‘yan kabilar Uighur (wee-goor) ‘yan tsiraru, wadanda ke da dangantakar kabila da Turkawa. Turkiyya na so ta kafa masana’antu a yankin na Xinjiang. Mr.Erdogan zai kammala ziyarar shi da Shanghai.