Bayanai sun nuna cewa hadarin ya auku ne yayin da wata mota da ta taso daga Gidin Dorawa suka yi taho mu gama da wata motar safa kirar makafolo. Yawancin fasinjojin dake cikin motar mata ne wadanda suka fito daga cin kasuwa. An ce motar na dauke da jarkoki na man fetur da kanazir. A kokarin kaucewa motar safar direban ya saki hannu sai ya afka daji inda ta buga itace nan take ta kama da wuta. Yawancin matan dake cikin motar suka kone. Nan take mata 13 sun mutu.
Wadanda suka samu suka tsira da rayukansu an garzaya da su babban aibitin garin Wukari yayin da kuma jami'an hukumar Road Safety ke hada alkaluman wadada hadarin ya rutsa da su. Mr. Peter Kigbo jami'in hukumar ya ce ya samu labarin hadarin amma yana jiran cikakken bayani.
Hadarin motoci a kan hanyoyin Najeriya ba wani abu sabo ba ne. Rashin hanyoyi masu kyau da tukin ganganci su ne umalubaisan yawan hadarin motoci.