Babbar jam’iyyar hamayyar kasar Ghana ta gabatar dan takaran ta a zabe mai zuwa,Nana Afuko-Addo mai shekaru 66, wanda kiris ya hana shi yin nasara a zaben fidda gwanin da aka yi tsakanin shi da shugaban kasar Ghana John Atta Mills a watan janairun shekarar dubu biyu da tara.
Da yammacin jiya asabar jam’iyyar New Patriotic Party ta gabatar da shi a zama dan takarar ta a zabe mai zuwa. A cikin wani jawabin da ya yi, shi kuwa ya yi alkawarin kai jam’iyyar ga nasara.
Ghana na daya daga cikin kasashen Afirka masu demokradiyar da ta girku da kyau fiye da kowa, tun bayan farfadowar siyasar jam’iyu da dama a kasar a shekarar 1992, an yi zabubbukan shugaban kasa har sau biyar a kasar.
Ana kyautata zaton cewa kasar za ta fara hakar mai kafin zabe mai zuwa, bayan tulin albarkatun man da aka gano a kasar.