Dubban 'yan Kenya sun shiga kuri'ar raba-gardamar da aka gudanar yau laraba a kan sabon tsarin mulki, wanda zai rage ikon shugaban kasa tare da kara karfin hukumomin jihohi da kananan hukumomi.
Gobe alhamis da maraice zuwa safiyar Jumma'a ake sa ran za a fara samun sakamakon wannan kuri'a.
Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a da aka gudanar kafin zaben sun nuna cewa mafi yawan 'yan Kenya sun kuduri aniyar goyon bayan sabon tsarin mulkin wanda ya kunshi tanade-tanade kamar ikon mallakar filaye da batun zub da ciki.
Jami'an Kenya sun yi alkawarin gudanar da zaben na yau laraba cikin yanayi na gaskiya da kwanciyar hankali fiye da zaben shugaban kasar da aka yi ta gardama kai a shekarar 2007.
Zarge-zargen magudi a wancan zaben sun haddasa mummunan yamutsin da ya kai ga mutuwar mutane fiye da dubu daya da dari uku.
Sabon tsarin mulkin da ake kuri'a kai yau laraba yana daga cikin yarjejeniyar raba-ikon da aka cimma a bayan zaben na 2007 da aka yi gardama kai.
Sabbin dokokin dake cikin tsarin mulkin zasu takaita yawan 'yan majalisar zartaswa, watau ministoci da makamantansu, da kawar da mukamin firayim minista tare da takaita ikon mallakar filaye ga wadanda ba 'yan asalin kasar ta Kenya ba ne.