Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Tana Zawarcin Gwamna Wamako Na Sokoto


Alamar sabuwar jam'iyyar 'yan hamayya ta APC
Alamar sabuwar jam'iyyar 'yan hamayya ta APC

Jigajigan jam'iyyar APC sun ziyarci jihar Sokoto domin neman Gwamna Wamako da magoya bayansa su shiga jam'iyyar.

Tawagar jam'iyyar APC data kunshi manyan jami'anta mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa Bisi Akande, da tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu, da tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da tsohon kakakin majaklisar wakilai tab tarayya Aminu Masari, sun gana da gwamna Wamako a kebe, kamin daga bisani su fito domin su yiwa magoya bayan gwamnan da suka hallara a fadar gwamnati jawabi.

Cikin jawabinsa, mukaddashin shugaban jam'iyyar Bisi Akande ya bayyana damuwar ganin hali da Najeriya ta shiga karkashin jagorancin jam'iyyar PDP wacce Gwamna Wamako yake ciki, jam'iyyar da Akande ya azawa laifin tabarbarewar harkoki cikin Najeriya.

Da yake magana da wakilin Sashen Hausa, Janar Buhari ya gayawa wakilin Sashen Hausa a yankin cewa suna jihar ne domin neman goyon baya ga jam'iyyar daga al'umar jihar sokoto ta hanun gwamna Aliyu Magatakarda Wamako. Da aka tambayeshi yaya zasu zawarci mutumind a yake cikin wata jam'iyya, janar Buhari yace ai gashi a fili irin rigimar da gwamnonin suke fama da shi da jam'iyyarsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG