Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar APC A Jihar Zamfara Ta Hana Mata Uku ShigaTakara


Yayin da 'yan siyasa a tarayyar Najeriya ke ci gaba da neman lasisin tsayawa takarar shugabanci, jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta haramtawa wasu mata uku tsayawa takara.

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta haramtawa wasu mata su uku shiga takarar kujerar majalisar dokoki ta tarayya da kuma majalisar dokoki ta jihar, to amma cibiyar National Democratic Institute mai rajin bunkasa harkokin demokaradiyya ta ce matakin tsagaro ne tsarin demokaradiyyar najeriya.

Hajiya Asabe Bala Kanoma wacce ta fito neman kujerar majalisar dokoki ta jihar Zamfara, mai wakilatar mazabar Maru ta daya da Malama Shafa’atu Salihu Labbo dake neman wakiltar mazabar Kaura ta arewa a majalisar dokokin ta jihar Zamfara, kana kuma da Hajiya Amina Iliyasu dake neman takarar kujerar tarayya ta Talatan Mafara/Anka a majalisar wakilai.

Sai dai za a iya cewa hakan dai wani koma baya ne ga yunkurin da cibiyar National Democratic Institute wato NDI keyi na ganin karuwar adadin mata masu rike mukaman sisaya a arewa da wasu sassan kudancin kasar.

Jam'iyyar APC A Jihar Zamfara Ta Hana Mata Uku ShigaTakara 5'24
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG