Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyun Adawa Sun Yi Zanga Zanga a Yamai


Dandazon magoya bayan gamayyar jam'iyun adawa ta FRDDR a Nijar yayin wata zanga zanga da suka gudanar a Yamai ranar 31 Disamba 2017
Dandazon magoya bayan gamayyar jam'iyun adawa ta FRDDR a Nijar yayin wata zanga zanga da suka gudanar a Yamai ranar 31 Disamba 2017

A wani mataki da suka dauka na nuna rashin gamsuwarsu da kamun ludayin gwamnatin shugaba Muhammadou Isufu, gamayyar jam’iyun adawa a Jamhuriyar Nijar ta gudanar da zanga zangar lumana a Birnin Yamai.

Jam’iyun kawancen adawa na FRDDR a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da zanga zangar lumana a yau Lahadi a birnin Yamai.

Gamayyar jam’iyun ta ce ta gudanar da zanga zangar ce domin jan hankalin hukumomi akan abinda ta kira "mulkin kama karyar" da ya jefa ‘yan kasar cikin kuncin rayuwa.

Magoya bayan jam’iyun sun yi tattaki daga wani dandali a Birnin na Yamai zuwa wani yanki da ke kusa da majalisar dokokin kasar.

“Ka san wannan shekarar ba a tabuka komai ba, sai zalunci sai rashin karatu sai rashin magani a likita (asibiti).. ga yunwa.” Inji Kakakin jam’iyar RDR ta kawance FRDDR, Alhaji Dudu rahama.

Sai dai jam’iya mai mulki ta PNDS tarayya, ta ce duk matsalolin da ‘yan adawan suka zayyana ba su da tushe ballantana makama.

“In ka dauki maganar kiwon lafiya aikin da aka yi a wannan fanni, yau ‘yan kasa sun kare tafiya Morocco ko Algeria neman magani.” Inji Kakakin jam’iya mai mulki, Assoumana Muhammadou.

Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG