Jami’an tsaron Faransa sun je Rwanda don su binciki ‘yan Rwanda da ke zaune a Faransa da ake zargin sun a da hannu a kisan kiyashin 1994.
Jean-Bosco Siboyintore, mai shugabantar sashen farauto madanda su ka gudu a ofishin masu gabatar da kara da ke Rwanda, ya gaya wa manema labarai cewa jami’an tsaron za su kasance a kasar na tsawon sati biyu, su yi binciken batutuwa da dama.
Jami’in y ace kasar Rwanda ta bayar da sammacin kama akalla ‘yan ruwanda 12 da ke zaune a Faransa.
Daya daga cikin wadanda ake zargin it ace Agathe Habyarimana, matar marigayi shugaba Juvenal Habyarimana. A na ganin kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban a watan Afiriluin 1994 shi ne ya haddasa kisan kiyashin da aka yi wa kimanin ‘yan Tutsi 800,000.
A na wannan binciken ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Faransa da Rwanda ke kara inganta. Rwanda ta yanke huldar jakadanci da Faransa a 2006 bayan da wani alkalin Faransa ya zargi shugaba Paul Kagame da bayar da umurnin kashe Mr. Habyarimana.