Shugaban Amurka Barack Obama ya bada sanarawar cewa a ran Alhamis 8 ga watan nan na Satumba ya shirya yin jawabin dalla-dalla ga Majalisar dokokin Amurka hanyar da Gwamnatinsa ke son bi domin kaiwa ga samar da ayyukan yi ga Amerkawa da yadda za’a kai ga sake farfado da tattalin arzikin Amurka.
Sai dai a wani abinda ake ganin ci gaba da tabarbarewar dangantaka a tsakanin manyan jami’yyun siyasa biyu na Amurka, shirya ranar yin jawabin sai ta zama abin cece-kuce inda Kakakin majalisar wakilai John Boehner, kuma jigon jam’iyyar Republican a majalisar dokokin Amurka yayi kukan cewa zai wahala a shirya zaman hadin gwiwar majalisar dokoki a kurarren lokacin da shugaba Obama ya fara shiryawa domin yiwa Majalisar jawabi don haka jinkirta da kwana guda.
Jiya Laraba, shugaba Barack Obama wanda dan jam’iyyar Democrat ne, yace ya amince da shawarar da kakakin majalisar wakilan Amurkan ya bayar, hakan ne yasa aka amince da yiwa majalisa jawabi a ran takwas ga watan Satumban. Shugaba Barack Obama yana mai cewa wajibi ne Amurka ta dauki mataki mai karfin da zai taimaka a farfado da tattalin arzikin Amurka da samarwa Amerkawa ayyukan yi, don haka yace akwai bukatar ganin samun hadin kan shugabannin majalisar dokokin Amurka.
Idan da ambi shirin tsaida ranar farko ta yin jawabin na Barack Obama, da kuwa an hadu da matsalar tinkarar muhimman abubuwa biyu, yin muhawarar Telbijin da manyan ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican zasu yi a daren, ga kuma zaman sauraren jawabin na shugaban kasa.