Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGER: Wasu 'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Amurka da Na Nijar Jiya Laraba


Sojojin Amurka da suke horas da sojojin Nijar
Sojojin Amurka da suke horas da sojojin Nijar

'Yan ta'addan kasar Mali dake yawan kutsawa kasar Nijar sun ketara cikin kasar din jiya Laraba a yankin Tilaberi inda suka kashe sojojin Nijar da na Amurka yayinda suke sintiri

An kashe sojojin Amurka na musamman uku da sojojin Jamhuriyar Nijar biyar, an kuma raunata wasu biyu, bayan da aka kai musu hari a jiya Laraba, yayin da suke sintiri a yankin Tilaberi dake kan iyaka da kasar Mali.

Rundunar sojan Amurka dake a nahiyar Afirka ta ce an kai harin ne a kusa da kan iyakar kasar Mali da Nijar, mai nisan kusan tazarar kilomita 190 daga Arewacin babban birnin Nijar, Yamai.

An dai kwashi sojojin da suka jikkata zuwa birnin Yamai, kuma suna cikin yanayi mai kyau, a cewar jami’an Amurka, wadanda basu da ikon yin magana kan faruwar lamarin.

An kaiwa sojojin harin ne a yankin da wasu mayakan kungiyar al-Qaida na yankin suke.

Rundunar sojan Amurka a nahiyar Afirka, ta ce dakarun Amurkan na musamnman suna Jamhuriyar Nijar ne domin bayar da horo ga sojojin Najeriya ta yadda zasu shawo kan matsalar ta’addanci a yankin, ciki har da wadanda suka tsallako iyaka daga kasar Mali suka shiga Nijar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG