Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Boko Haram Sun kai Hari A Shetimari Cikin Nijar


Sojojin Nijar a sansanin soja dake Bosso
Sojojin Nijar a sansanin soja dake Bosso

Kungiyar boko haram takai hari a garin Shatemeri dake cikin jamhuriyar Niger har ta kashe dan karamin yaro guda.

‘Yan boko haram sun kai hari a garin Shetimari dake jihar Difa a Jamhuriyar Nijar. Wannan harin yayi sanadiyyar hasarar rai.

Wakiliyar sashen Hausa Tamar Abari ta ce a zantawar ta da wani dan taliki da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana mata cewa maharan sun kawo hari ne bayan sallar magariba.

Yace ba zato ba tsammani da magariba sai suka ga motoci da yawan su ya kai 12 sun bi ta inda sojoji suke kuma kawo lokacin da yake bayani bai san halin da suke ciki ba.

Yace a cikin garin ba wani wanda ya jikkata, sai dai da aka tambaye shi batun hasarar rai sai yace harsashi ya gilma kuma ya sami wani dan karamin yaro.

Yaci gaba da cewa maharan basu shigo cikin gari ba, daga wajen gari ne sukayi dukkan abinda suka yi, kuma jami'an gwamnati ba su kawo ziyara a inda wannan lamari ya faru ba.

Ga Tamar Abari da Karin bayani 3’12

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG