Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Amurka Na Kokarin Ba Kasashen Kawancen NATO Tabbaci Amurka Ba Zata Bijire Ba


Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Donald Trump

Yayinda kasashen kawancen NATO ke shirin yanke shawarar takawa Rasha birki a taron kolinsu suna tababa akan shugaban Amurka dake kokarin ganawa da shugaban kasar Rasha din, Vladimir Putin

Jami'an gwamnatin Amurka na ta kokarin ba da tabbaci ga sauran kasashen Yammacin duniya cewa,

Shugaba Donald Trump zai jaddada kudurin Amurka na tinkarar Rasha a babban taron NATO na gaba da kuma ganawar da zai yi da Shugaban Rashar Vladimir Putin.

Shugabannin da za su halarci babban taron na NATO za su yanke shawarar kara kaimi da kuma matakan tsaro don taka ma Rasha burki, a yinkurinta na "kawo rarrabuwa tsakanin kasashenmu masu bin tafarkin Dimokaradiyya" da kuma saba ma 'yarjajjeniyar da aka cimma kan Matsakaicin Makamin Nukiliya (INF, a takaice), a cewar wakilin Amurka na dindindin a kungiyar ta NATO, Kay Bailey, a hirarsa ta wayar tarho da manema labarai na Fadar White House a jiya Alhamis.

Kwanan nan Trump ya aika da wasu wasiku masu kakkausan lafazi ga wasu Shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar ta NATO da dama, ciki har da Belgium da Canada, da Jamus da Norway, inda ya gargade su kan gajiya da hakuri da Amurka ke yi kan rashin biyan nasu kason kudaden gudanar da harkokin tabbatar da tsaro a karkashin NATO.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG