Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutum 4 a Mogadishu

Yadda jami'an lafiya suka tafi da wani wanda ya samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai kwanakin baya
Yadda jami'an lafiya suka tafi da wani wanda ya samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai kwanakin baya

Rahotanni sun ce wani dan kunar bakin wake ya hallaka a kalla mutane 4 a wani shahararren gidan cin abinci da jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati ke zuwa sosai a Mogadishu.

Wasu mutane da dama sun samu raunuka a wurin cin abincin na Lul Yamani dake tsakiyar Mogadishu, babban birnin Somali.

Wasu jami'an tsaro kusa da wata motar da wani mai kunar bakin wake ya hallaka
Wasu jami'an tsaro kusa da wata motar da wani mai kunar bakin wake ya hallaka

'Yan sanda sun bayyana cewa dan kunar bakin waken ya tayar da bomb din dake jikin shi ne bayan da mai tsaron gidan abincin ya hana shi shiga.

Duk da cewa babu wanda ya dau alhakin kai harin, ana zargin mayakan Al-shabab da kai harin saboda tarihinsu na kai hari kan jami’an tsaro.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG