Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Al-Shabab Ya Halaka Mutum 7 a Somalia


Akalla mutum bakwai ne suka mutu a wasu hare-hare guda biyu da mayakan Al Shabab suka kai a Somalia a karshen makon da ya gabata.

Hari mafi muni cikin hare-haren biyu, shi ne wanda aka kai a garin Wanlaweyn mai tazarar kilomta 90 da ke yammacin birnin Mogadishu, inda wani bam hadin-gida da aka dasa a kusa da gidan wani jami’in soji ya tashi.

Jim kadan kuma wani bam na biyu ya tashi yayin da mutane suka yi cuncurundo a inda bam din farko ya tarwatse.

Mutum biyar ne suka mutu ciki har da matar sojan wanda a lokacin da lamarin ya faru ba ya gida.

Mataimakin gwamnan yankin Lower Shabelle Ahmed Yusuf ya tabbatarwa da sashen Somali na Muryar Amurka da mutuwar mai dakin sojan.

Ya kuma kara da cewa, an kama mutane da dama da ake zargin na da hannu a hare-haren yayin da ake kan gudanar da bincike.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG