Firayim Minista Abdelmalik Sellal ya tabbatar da labarin jiya Asabar, tare da cewa halin da Shugaban ke ciki ba mai hadari ba ne. Ya ce Shugaban ya yi fama ne da ‘yar toshewar magudanar jini na wani dan lokaci a jiya Asabar kuma ya na kan murmurewa, kafin gwaje-gwajen da ke biye.
Mr. Bouteflika ya shugabanci Aljeriya tun 1999, kuma ana ganin ya na fama da rashin lafiya cikin ‘yan shekarun nan. Ba kasafai ya kan shiga jama’a ba.
Mr. Boutiflika ya kaddamar da sauye-sauyen siyasa cikin 2011, sanadiyyar wata gagarumar zanga-zangar jama’a, da ke da alaka da zaburowar juyin juya halin Larabawa.
Aljeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da su ka fi arziki, kuma daya ce daga cikin kasashen da su ka fi sayar ma Nahiyar Turai iskar gas.