Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan sanda a Bangladesh sun ce sun kama mai ginin rukunin kamfanonin nan da ya ruguje makon jiya, ya hallaka mutane sama da 350


Savar, Dhaka, Bangladesh, Afrilu 28, 2013
Savar, Dhaka, Bangladesh, Afrilu 28, 2013

‘Yan sanda a Bangladesh sun ce sun kama mai ginin rukunin kamfanonin nan da ya ruguje makon jiya, ya hallaka mutane sama da 350

‘Yan sanda a Bangladesh sun ce sun kama mai ginin rukunin kamfanonin nan da ya ruguje makon jiya, ya hallaka mutane sama da 350.

Yan sanda sun fadi yau Lahadi cewa sun damke Mohammed Sohel Rana a kusa da kan iyakar Indiya. Rana ya yi layar zana ne tun bayan da ginin ya ruguje ranar Laraba.

‘Yan sanda sun ce Rana da manajojin kamfanin sun yi watsi da gargadin da aka yi a hukumance, cewa mutane su fa kaurace wa ginin bayan da kwararrun dubagari su ka gano tsagu a ginin ranar Talata.

A yau Lahadi ma masu ayyukan ceto sun zakulo akalla mutane hudu da ransu daga baraguzan ginin.

Masu ayyukan ceton gaggawa sun yi ta amfani da kayan aiki da hannu, wajen neman wadanda har yanzu ke raye da kuma gawarwaki, to amma jami’ai sun ce sun kusa su fara amfani da katafila. Da dai hukumomi sun jinkirta amfani da manyan katafiloli ne, saboda kare wadanda ke raye cikin tarkajen ginin.

Jiya Asabar ‘yan sanda sun ce sun kama wasu mutane 6 dangane da rugujewar ginin. Wadanda aka damke din sun hada da wasu injiniyoyin gwamnati biyu da su ka amince da tsarin ginin da wasu shugabannin kamfanin biyu – wato da babban Manajan kamfanin na New Wave Apparels da kuma Ciyaman din.

Rukunin ginin da ya ruguje a bayan birnin Dhaka din na kunshe ne da masaku biyar na kayan tufafi.
XS
SM
MD
LG