Wakilin Sashen Hausa, Ibrahim Abdulaziz, yace a yanzu, jama'a da dama daga Yola, babban birnin Jihar, da wasu sassan, su kan dauki hayar motoci da wasu ababen hawar zuwa wasu garuruwa da wurare a tsallaken iyaka a Jihar Taraba, domin su samu zarafin yin magana da 'yan'uwa ko abokan huldar cinikayyarsu a wasu sassan Najeriya da duniya.
Wasu kwararru kamar 'yan kwangila da malamai, su ma su na barin jihar a saboda wannan hali na rashin hanyar tuntubar 'yan'uwansu a kasashen waje. Gwamna Murtala Nyako, yace wannan lamarin ya shafi shahararriyar jami'ar nan ta ABTI-American dake Jihar, wadda malamanta suke barin gari a saboda halin da aka shiga.
Sai dai kuma a wani lamarin, wasu masu sana'a a irin garuruwan da mutane ke zuwa domin su yi wayar, sun bayyana wannan abu a zaman wani abin alheri a gare su, a saboda samun karin masu ciniki. Wata mai toyawa da sayar da doya ta ce a yanzu, tana samun kasuwa sosai a saboda dimbin jama'a dake zuwa.
'Yan jarida da dama su ma sun koka a saboda wahalar da suke samu wajen samo labarai ko aika su ga kamfanoninsu.
Ga cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola, kan wata guda da shiga dokar-ta-baci a Jihar Adamawa.