A wani matakin da ya ba kowa mamaki a garin na Maiduguri, an ga matasan wadanda suka yi kundumbala su na yawo kwararo-kwararo a garin Maiduguri, su na tinkarar 'yan bindiga, su na masu fadin cewa abin ya kawo musu wuya, an hana ma iyayensu barci, an kashe musu 'yan'uwa.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka ya ce wannan lamarin harkokin tsaro a garin Maiduguri ya canja salo, ganin yadda jama'a a yanzu suke yin kukan kura su abka kan 'yan bindigar da suka yi ido hudu da su.
Yace a yanzu kusan dukkan unguwannin dake cikin Maiduguri da ma wasu sassan jihar Yobe makwabciyarta, jama'a sun fara kafa irin wadannan kiungiyoyi na farauto 'yan bindigar da a wasu lokutan a kan lallasa sosai, kafin a damka su ga jami'an tsaro.
Matasan da suka tattauna da wakilin Sashen Hausa a garin na Maiduguri, sun roki jama'ar gari da su taya su da addu'a, ita kuma gwamnati ta taimaka musu da makamai domin su niya gudanar da wannan aikin sa kai da suka runguma.
Ga rahoton tattaunawar da wakilinmu yayi da wasu matasan a tsakiyar garin Maiduguri...