Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikar Sarkin Kano Shekaru 50 Bisa Gadon Sarauta


Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero

Jihar Kano ta arewacin Nijeriya na nan na kan shirye-shiryen bukin cikar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero shekaru 50 bisa gadon sarauta.

Masarautar Kano da gwamnatin jihar Kano sun dukufa wajen shirye-shiryen cikar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero shekaru 50 bisa gadon Sarauta.

A hirar da wakilinmu a Kano, Muhammad Salisu Rabiu ya yi da Mai Martaban, ya ce ya na mai matukar farin ciki da yadda jama'ar Kano ke cigaba da nuna masa kauna, duk da canje-canjen da zamani ya kawo. Ya ce Allah shi ke da zamani, saboda haka ya na mai na'am da duk wani sauyin da Allah ya kawo. Ya yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya da cigaba ma Nijeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Alhaji (Dr.) Ado Bayero ya zama Sarkin Kano na 13 a sarautar Fulani ranar 15 ga watan Yunin 1963.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG