Martanin ya bayyana ne a wata sanarwa da Hon. Debo Ologunagba, kakakin PDP ya fitar wa manema labarai, inda ta bayyana rashin jindadi da rashin amincewa da yadda ake tafiyar da kalubalen tsaro da ake fuskanta a jihohi daban-daban.
Jam’iyyar PDP ta ce Shugaba Tinubu ya gaza a jawabinsa na sabuwar shekara wajen jajantawa kan kashe-kashen da ake yi a Filato da sauran jihohin kasar nan, inda ta caccaki jawabin da cewa bai dace da shugaban kasa ba.
PDP ta kuma zargi Shugaba Tinubu da yin watsi da muhimman batutuwa da suka shafi kasa kamar rashin tsaro, durkushewar ababen more rayuwa, gurbacewar masana’antu, hauhawar farashin kayayyaki, da rashin aikin yi.
Jam’iyyar ta kara da cewa, “Shugaba Tinubu bai ce uffan ba a jawabinsa na sabuwar shekara na kisan kiyashin da ‘yan ta’adda suka yi wa ‘yan Najeriya sama da 200 a jajibirin Kirsimeti da kuma kashe ‘yan kasa sama da 5000 a Filato da sauran jihohin tarayya da ke karkashinsa tun a ranar 29 ga watan Mayun shekaran 2023. Wannan wani irin shugaba ne?"
Da take bayyana wasu korafe-korafe na musamman, PDP ta nuna rashin jin dadinta da yadda tattalin arziki ke tabarbarewa a kasa, yadda farashin mai ya haura daga naira 167 zuwa kimanin naira 700 kowace lita tun hawan Shugaba Tinubu karagar Mulki, da faduwar darajar Naira, da kuma fifita kashe kudi a cikin kasafin kudin 2024 ba tare da bayyanannun tsare-tsare na bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ba.
Bugu da kari, PDP tayi korafi da tafiye-tafiyen da ya ke yi a kasashen waje tare da abokan siyasa, a cewar ta, hakan bazai “taimaka wa kasarmu ba”.
Jam’iyyar ta zargi Shugaba Tinubu da ta’azzara abubuwa ta hanyar kokarin raunana wasu muhimman sassan gwamnati, kamar Majalisar Dokoki ta kasa da kuma Hukumar Zabe ta Kasa, wanda PDP ta bayyana hakan bai dace ba.
Jam’iyyar ta adawa ta cigaba da zargin Shugaban inda ta ce, yana jawo wa ‘yan Nijeriya matsaloli da dama da gangan, kuma abin da ya yi yana kawo wa mutane wahala.
PDP tace a jawabin na Shugaban, ya kamata ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri karara kuma PDP tana son Shugaban kasa ya bayyana inda duk kudaden kasa ke tafiya, musamman wajen cire karin kudin man fetur. Suna fargaba da zargin cewa wannan kudi na iya shiga aljihun wasu shugabannin siyasa.
A karshe, jam’iyyar PDP ta bukaci Majalisar Dokokin Kasar, kungiyar masu kafa doka da su yi aikinsu da kyau, su kuma sanya ido a kan shugaban kasar don tabbatar da cewa yana yin abubuwa yadda ya kamata.
Jam’iyya mai mulki ta APC ta maida martani ta hanun mai magana da yawun jam’iyya na kasa, Malam Bala Ibrahim, inda ya shaidawa Muryar Amurka cewa babu abinda ke damun ‘jam’iyyar PDP illa rudani saboda shan kaye da sukayi a zaben bara na shugaban kasa.
Ibrahim ya bayyana cewa jawabin shugaban na Najeriya dauke yake da sakonni masu muhimmanci da tsare-tsaren gwamnati don habbaka tattalin arziki kamar yadda shugaban ya fitar da sabon tsare tsare na bangaren noma hekta dubu 500,000 na gonaki a fadin kasan nan domin noman masara, shinkafa, alkama, gero da sauran kayan amfanin gona. Da kuma kaddamar da noman rani da fili mai fadin hekta dubu 120,000 a jihar Jigawa a watan Nuwamban da ta gabata, wanda duk wadannan matakai ne na alheri da Shugaban Kasa ke yi.
Da yake martani kan zargin da PDP ta yiwa Shugaba Tinubu na rashin ambato da nuna alhini da hare-haren da aka kai jihar Filato a lokacin bikin Kirsimeti, Bala Ibrahim yace,
“Babu shakka Shugaban Kasa ya nuna alhini da jajantawa ga irin ta’addanci da hare-hare da ‘yan ta’adda ke kaiwa a fadin kasan nan, kuma Shugaban ya nuna damuwarsa matuka.
"Najeriya muna da sama da mutane miliyan dari biyu banda wadanda suka rasa rayukan su, idan yanzu aka ce Shugaban Kasa sai yabi kowa dai-dai ya ambace shi a jawabinsa, ai yayi kadan a jawabin minti talatin.
"A cikin jawabin da Shugaban Kasa ya bayyana halin da tsaro ke ciki, kuma ya jaddada kokarin da gwamnati take yi musamman a bayan fage wajen ganin magance matsalar. Shugaban Kasa da kanshi ya bayyana cewa a yanzu gwamnati ba za ta buga kirji tace ta magance matsalar tsaro ba, amma tana iya kokarin ta".
Haka zalika, ya jajantawa illahirin ‘yan Najeriya game da matsalar tsaro, saboda harkar tsaro batu ne da ya shafi dukkan kasa ba wani sashi ba, saboda haka babu bukatar ambaton wani sashi wajen jajantawa a jawabin shugaban kasa, jam’u da yayi a jawabinsa hakan ya wadatar” in Bala Ibrahim
Da yake maida martani game da hauhawan farashin mai da faduwar darajar naira da PDP ke zargin akwai sakacin gwamnati a ciki, mai magana da yawun APC na kasa ya bayyana cewa “kusan duk duniya ne baki daya, hatta kasashen da suka cigaba irin Amurka, suna fama da hauhawan farashin mai, amma duk da haka gwamnatin Tinubu na cigaba da daukan matakan da ya kamata wajen rage radadin cire tallafin na mai kuma abin a yaba mata ne”, in ji shi.
Da yake tsokaci game da zargin da PDP tayi na inda kudin tallafin man fetur da aka cire ke zuwa, Ibrahim yace,
“Batun tallafi da gwanati ta cire wanda dama can mutane ne kalilan ke amfana da shi suna barin sauran ‘yan kasa cikin wahala, yanzu gwamnati ta karkata wannan kudi izuwa fannoni masu muhimmanci wanda dukkanin abubuwan na kunshe a cikin kasafin kudi na wannan shekara 2024 wanda zai amfani kasa
Kuma batun wai kudaden an karkatasu zuwa wasu shuwagabanni na APC, "ba komai bane illa yarfe na siyasa da kage. Ta yaya za’a bayar da kudin, abinda komai yana tsare cikin doka kuma dole sai an saka su cikin kasafin kudin kasa, idan da gaske suke sai su fada mana su waye ake baiwa kudaden a APC? Su fada mana, wannan kage ne kawai da zafin shan kaye a zabe da PDP ke fama dashi har izuwa yau”
Ya cigaba da cewa, idan PDP bata manta ba ai tun kafin zuwan shugaba Tinubu aka zartar da dokokin zabe wanda tsarin da ake bi kenan.
Dandalin Mu Tattauna