Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Ghana: Dan Takara Ya Yi Alkawarin Kara Kwanakin Hutun Sallah In Ya Yi Nasara


Dan takaran Shugaban Kasa a karkashin tutar babbar jam’iyar adawa ta NDC a zaben 2024, kuma tsohon Shugaban Kasa, John Dramani Mahama,
Dan takaran Shugaban Kasa a karkashin tutar babbar jam’iyar adawa ta NDC a zaben 2024, kuma tsohon Shugaban Kasa, John Dramani Mahama,

Dan takaran Shugaban Kasa a karkashin tutar babbar jam’iyar adawa ta NDC a zaben 2024, kuma tsohon Shugaban Kasa, John Dramani Mahama, ya ba da tabbacin cewa, a shirye yake ya ba Musulman kasar karin hutun bukukuwan Idi, idan jam’iyarsa ta samu nasara a zabe mai zuwa.

Hakan ya biyo bayan wata bukata da Shugabanin Musulmai a kasar Ghana suka bayyana a watan Oktoban bara su na neman karin hutun bukukuwan Sallah.

Tsohon Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne a taron shekara shekara na kungiyar Ghana Muslim Mission karo na 63 a birnin Kumashi, inda ya jaddada bukatar gyara Dokar Hutun Jama’a na 2001.

Yace: Aniyarmu ce mu warware matsalar da wasu ‘yan uwa musulmi da ba sa jin dadin hutun jama’a na karshen azumin watan Ramadan saboda dokar kwanaki 29 ko 30, na ganin watan. Don haka, za mu kara hutu a cikin bukukuwan Eid-el-Fitr.

"Insha Allahu idan an zabe mu, za mu kara hutu a bikin Eid-el-Fitr. Kuma za mu yi hakan ne ta hanyar sake fasalin Dokar Hutu ta Jama’a ta yadda Ghana za ta ci gaba da gudanar da bukukuwan hutu iri daya a kowace shekara”, a cewarsa.

Garba Osman, dan jarida kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya bayyana jin dadinsa ga wannan alkawari duk da cewa wasu na ikirarin cewa domin siyasa ne ya yi wannan alkawarin.

Mahalarta taron shekara shekara na kungiyar Ghana Muslim Mission karo na 63 a birnin Kumashi.
Mahalarta taron shekara shekara na kungiyar Ghana Muslim Mission karo na 63 a birnin Kumashi.

"Musulmai sun jima suna neman karin kwana daya ga hutun Sallar Eid-el-Fitr shi wannan alkawari da dan takaran jam’iyar adawa, tsohon Shugaban Kasa ya yi na karawa Musulmai hutu, ko da yake wasu na cewa siyasa ce, amma ai ganimar siyasa itace biyawa al’umma bukata. Tun da yace zai biyawa Musulmai bukatarsu, ina ganin daidai ne kuma bai sabawa ra’ayi na ba" in ji dan jaridan.

Kafin John Mahama ya yi wannan alkawari, dan Majalisar Dokoki mai wakiltar mazabar Madina, Francis-Xavier Sosu, a ranar 14 ga watan Disambar 2023, shi ma ya mika wani sabon kudiri na mambobi masu zaman kansu don yin kwaskwarima ga Dokar Hutun Jama'a ta kasa ta 2001, doka ta 601, wanda a ciki akwai karin ranakun hutu biyu ga Musulunci; wato ranakun Tashreeq da Haqq, ranakun jajibirin Babbar Sallah da Karamar Sallah.

Kamar yadda dokar hutu na Ghana ke cewa, Ministan Cikin Gida na sanar da hutun jama’a kwanaki biyar kafin lokacin, kuma sabili da yadda ake samun sabanin kwanakin watan Ramadan; wato kwanaki 29 ko 30, ya sa ana yawan jinkirta karamar Sallah da kwana daya a duk lokacin da aka yi azumi 29, wanda ya sa ake samun sabani tsakanin bangarorin Musulman Ghana.

“Wannan na daga cikin dalilan da ya sa Musulmai za su so matuka, a kara ranakun hutu a bukukuwan Sallah.

“Idan azumi na da 25 ya kamata a bayyana hutu ga al’umma, domin haka, zai yiwu a sa hutun ranar 30 ga watan Ramadan da kuma 1 ga watan Shawwal; hakan zai magance matsalar da muke fuskanta” a cewar wani mahalarta taron, Alhaji Mamoun Ibrahim Jawula.

Alhaji Mamoun ya kara da cewa, ga babbar Sallah kuma, da yake mafi yawan Musulmai na azumi a ranar Arafa, kuma ranar Sallah a yi yankan layya. Domin haka, idan an samu kwanaki biyu, za a iya amfani da kashegarin a yi rabon nama ga jama’a.

Haka kuma, al’ummar Musulmai sun yi marhaba da wannan kuduri, da Kuma Kungiyar Majalisar Sarakunan Musulmai da Limamai na kasa ko (NACOKINS) a takaice sun bayyana goyon bayansu ga kudirin, tare da yabawa dan majalisa Francis-Xavier Sosu bisa ga jajircewarsa kan kudurin a wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin Tamale dake yankin Arewa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG