Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Hudu Daga Cikin 'Yaran Da Suka Makale Cikin Kogo A Thailand


Jirgin helicopta da ya dauki yaran da aka ceto zuwa asibiti
Jirgin helicopta da ya dauki yaran da aka ceto zuwa asibiti

Rundunar mayakan ruwan kasar kasar Thailand tace an ceto a kalla yara hudu daga cikin a ‘yan wasan kwallon kafa goma sha biyun nan da kocinsu, da suka makale na tsawon sama da makonni biyu a kogo da ruwa ya mamale.

Gwamnan lardin Chiang Rai, Narongsak Osatanakorn, shugaban aikin ceto yace masu nikayya suna bukatar a kalla sa’oi goma su sake shirin rukunin aikin ceto yaran na gaba kuma ana kyatata zaton komi zai tafi da kyau fiye da yadda aka zata.

An kai yaran hudu da aka ceto asibiti. Tun farko jagoran aikin masu aikin ya bayyana cewa, "A shirye muke. Yauce ranar gudanar da wannan aikin. A daidai karfe uku na rana agogon GMT kwararrun nikayya goma sha uku suka shiga kogon suka fara aikin ceto rayukan ‘yan kwallon. Tawagar ta hada da kwararrun nikayya na rundunar mayakan ruwan Thai biyar. Sun tsara yadda zasu shiga kogon da kuma aikinda kowanne dayansu zai yi."

Tawagar ta kunshi kwararrun ‘yan kasashen ketare goma sha uku da kuma fitattun masu nikayya na kasar Thailand biyar, wadanda suke da kwarewar tunkarar kowanne irin yayani da zasu fuskanta.

Kwararrun masu nikayya biyu zasu raka kowanne yaro. Jami’ai sun ce ana kyautata zaton za a dauki kwanaki biyu zuwa hudu kafin a fito da dukan yaran.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG