Bayan da kotun kolin kasar Kenya ta soke zaben shugaban kasa da aka yi cikin watan da ya gabata, hukumar zaben kasar mai zaman kanta da ake kira IEBC a takaice, ta bada sanrwa ajiya litinin da yamma cewa za a yi wani sabon zaben shugaba kasa ranar 17 ga watan Oktobar wannan shekarar, idan Allah ya kaimu.
Amma jagoran ‘yan adawa Raila Odinga da ‘yan jam’iyyar sa sun fada yau Talata cewa sun fi sona yi zaben ranar 24 ko 31 na Oktoba, akan cewa dole ne a sami isasshen lokaci don tattaunawa da hukumar zaben kasar,a duba batutuwan da suka sa ake neman sake yin wani zaben .
Odinga ya ce “bamu shirya yin zabe ranar 17 ga watan Oktoba ba, ba tare da tabbacin doka ba saboda bai kamata a sake yin kuskure har sau biyu ba,kuma a sa ran samun wani sakamakon kirki.
Odinga ya kara da cewa akwai bukatar a cire wasu manyan jami’an zabe ko kuma ma a hukunta su maimakon a barsu su sake kula da wani sabon zaben.
Facebook Forum