Baya ga tsadar rayuwa da al'ummar Najeriya ke fama da shi, yanzu kuma wani abu da ke ci wa ƴan Najeriya tuwo a kwarya shi ne karin kudin makarantun ‘ƴa’ƴansu.
Kusan kuɗin makarantun jami'o'in Tarayya ya ruɓanya kansa, kuma hakan ne ya sa Shugaban Malaman Jami'o'in Gwamnatin Tarayya, ya yi togaciya game da makomar karatun ƴaƴan talakawa.
Hakan ya sa wannan batu ya zama wata sabuwar barazana ga karatun yara ɗalibai, kamar yadda shugaban Malaman jami'o'in tarayyar Najeriya ta ASUU Farfesa Emmanuel Osadeke ya shaida.
Farfesa Osadeke, ya ce "kaso 40 zuwa 50 na ɗaliban jami'o'in tarayyar Najeriya za su daina zuwa makaranta nan da shekaru biyu masu zuwa, idan har aka ci gaba da ƙara kuɗin karatun jami'a".
Farfesan, ya ƙara da cewa "yawancin ɗaliban da ke jami'o'in gwamnatin tarayya, ƴaƴan talakawa ne, wanda kudin shigarsu a wata bai wuce Naira dubu 30 zuwa dubu 50 ba, kazalika za su biya kuɗin hayan gida da ma na tafiye-tafiye, a hakan ake ganin za su iya biyan kudin makaranta Naira dubu 300?"
Osadeke, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta duba wannan lamari kuma ta ƙarawa harkar ilimi kaso daga cikin kasafinta na shekara mai zuwa daga kaso 3.8 zuwa kaso 15.
A hirarsa da Muryar Amurka, Shugaban Malaman Jami'o'i Tarayya ta ASUU reshen jami'ar tarayya ta Kashere, Dakta Shehu Elrasheed, ya bayyana cewa wannan batun hauhawar kuɗin makarantun jami'o'in tarayya ka iya tilastawa jami'o'in rufe kansu.
Iyayen yara ɗalibai da ke jami'o'in Najeriya, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da su duba wannan lamari, a kuma sake lale game da hauhawar kuɗin makarantun ta yadda za'a samu sauki da yaran talakawa za su ci gaba da karatu.
Idan za'a iya tunawa, a baya-bayan nan an jiyo Ministan Ilimin Najeriya Farfesa Tahir Mamman, yana cewa gwamnatin tarayya tana yunƙurin bai wa jami'o'inta ƴancin cin gashin kai.
Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna