Shugaban kasar Madagascar,ya bijirewa sojoji dake ikirarin juyin mulki,yace ba zai yi murabus ba. Andry Rajoelina ya yi magana da manema labarai laraban nan a babban birnin kasar,jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a zaben raba gardama kan sabon tsarin mulkin kasar.
Yace sojojin sun yi barazanar halaka shi idan bai yi murabus ba, amma ya kara da cewa “bana tsoron barazana.”
Duk da haka shaidu sun bada labarin har yanzu gwamnatin Rajoelina ce da iko kan cibiyoyin gwamnati,bayan da sojojin suka yi ikirarin kwace iko a kasar,a bayani da suka yi a barikin soja dake kusa da tashar jiragen sama da ake kira Antananarivo.
Wani gungun sojoji su kamar ashirin, sun gayawa manema labarai a laraban nan cewa sun rusa dukkan ciboyoyin gwamnatin kasar,sun kafa kwamiti da zai tafiyar da mulkin kasar.
Kome yana tafiya cikin lumana a babban birnin kasar,kuma aka ci gaba da zaben raba gardaman cikin tsanaki.
Amma can da rana ance jami’an tsaron kasar sun kara da ‘yan zanga zanga dake kyamar gwamnati a wani barikin soja,inda bijirarrun sojojin da suka ayyana juyin mulkin suke.
Rahotanni da aka samu daga sansanin, sun ce daruruwan masu zanga zanga sun kafa shingaye da nufin hana sojojin shiga barikin.
Kamfanin dillancin labaran Reuters yace jami’an tsaro sun yi amfani da borkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga zanga.