Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana mutumin a matsayin Khalil Yahya Anis, mai shekaru 20.
Sojojin Isra'ila sun ce an yi wa sojojin nata luguden wuta a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a birnin Nablus, kuma suka mayar da wuta.
Sojojin Isra'ila sun kasance a yankin domin rusa gidan wani Bafalasdine da ake zargi da kashe wani sojan Isra'ila a bara.
Rikicin na ranar alhamis shi ne na baya bayan nan a cikin watannin da aka kwashe ana tashe tashen hankula da suka hada da hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare a yammacin gabar kogin Jordan, da kuma hare-haren 'yan gwagwarmayar Falasdinu. Akalla Falasdinawa 159 da Isra’ilawa 20 aka kashe.