Sai dai rahotanni daga kafafen sadarwar na kasar Iran na nuni da cewa, wadansu masu tsats-tsauran ra’ayi kalilan sun yiwa Amurka allah wadarai, wadansu kuma suka rika jifar ayarin shugaban kasar har da takalma lokacin da yake barin tashar jirgin sama ta Tehran yau asabar.
Mr. Rouhani ya koma gida ne bayan halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.
Kafin ya bar New York, jiya jumma’a, Mr. Rouhani da Mr. Obama suka yi magana ta wayar tarho na tsawon mintoci goma sha biya. Wannan ce tattaunawa ta farko kai tsaye da shugabannin Iran da na Amurka suka yi cikin kusan shekaru talatin da biyar, abinda wadansu suke gani a matsayin wata ci gaba ta warware takaddamar diplomasiya tsakanin kasashen biyu.
An daina duk wata huldar diplomasiya tsakanin amurka da Iran ne bayan juyin juya halin daular Islaman a shekara ta dubu da dari tara da saba’in da tara da ya kawo karshen masarautar da kuma matakin da masu zanga zanga suka dauka na mamaye ofishin jakadancin Amurka da yin garkuwa da Amurka na tsawon sama da shekara daya.
Dandanlin sadarwar twitter na Mr .Rouhani ne ya sanar da tattaunawar ta tarihi.
Mr. Obama yace shugabannin kasashen biyu sun tattauna a kan yunkurin cimma matsaya a kan shirin nukiliya na kasar Iran.