Wani babban kwamandan kasar Parisa, wato Iran, ya ce gwamnatin kasar ta yi daya-daya da jirgin saman leken asirin Amurka, sun karanci fasahar da aka yi amfani da ita, kuma har sun fara kwaikwayon fasahar su kera irin shi. A bara sojojin kasar Iran su ka kama jirgin saman leken asirin na Amurka.
A yau Lahadi kafofin yada labaran kasar Iran su ka ruwaito janar Amir Ali Hajizadeh, shugaban sashen kula da kere-keren ababen tashi sararin samaniya a kakkarfar rundunar jami’an tsaron juyin juya halin kasar ta Iran, ya na cewa haka kuma kwararrun masana na ciro bayanan da ke tattare a cikin jirgin saman samfurin RQ-170 Sentinel, wanda aka kama a gabashin kasar Iran a cikin watan Disemban shekarar da ta gabata.
Jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa jirgin saman leken asirin ya bace mu su. Amma sun ce zai yi wuya Iran ta iya samun wani bayani ko fasahar da aka yi amfani da ita wajen kera jirgin saman saboda matakan kare sirrin bayanan leken asirin da ake dauka a kan irin wadannan jiragen sama da ake turawa yankunan abokan gaba.
Hajizadeh ya ce jirgin saman na cike da harufan sadarwar sirri, amma ya ce sun gano bakin zaren, sun fahimci komi, sannan ya ce yanzu haka dai babu sauran wani boyayyen abu a cikin jirgin saman na leken asiri.
Ya ce an ciro wani bayani na hakika daga cikin jirgin saman wanda ya nuna cewa ya yi shawagi a sararin samaniyar maboyar shugaban al-Qaida Osama Bin Laden a kasar Pakistan, makonni biyu kafin a yi mi shi kisan gilla.