Wani babban kamfanin hada-hadar kudi da cinikayya a duniya ya bada labarin zai katse hulda da bankunan Iran, wadanda tarayyar turai ta azawa takunkumi, a ci gaba da kokarin da kasashen yammacin duniya suke yin a hana Iran zarafin sarrafa shirin nukiliyarta.
Kamfanin mai cibiya a Belgium yace zai mutunta umurnin tarayyar turai na katse hulda da kamfanonin hada-hadar kudin Iran daga gobe Asabar.
Matakinda aka dauka jiya Alahamis ya biyo bayan shawararda majalisar turai ta yanke na kara matsin lamba kan kamfanonin Iran da ake zargi suna da nasaba da shirin nukiliyar kasar, da kasashen yammacin duniya suke zargi Iran tana shirin kera makaman nukiliya ne, zargi ta Farisa ta musanta.
Kamfanin da ake kira da lakanin Swift kusan duk wani banki a duniya yana aiki dashi domin aikewa da sakonni gameda cinikayya da aikewa da kudi. Babban jami’in kamfanin Lazaro Campos ya kira matakin da cewa “wadda ba a taba dakan irinsa ba a tarihi.
Iran bata maida martani kan wan nan mataki ba.
Daukan wan nan mataki baki daya zai hana Iran zarafin mu’amalalar kudi da sauran kasashen duniya. Kasashen yammacin Duniya suna fatan hakan zai sa Iran ta tsaida shirin Nukiliyarta.
Ma’aikatar kudin Amurka tayi maraba da wan nan mataki, tana mai cewa hakan zai kara maida cibiyoyin kudin Iran saniyar ware.