Kasar Iran a bayyana cewa ta dakatar da saida danyen manta ga Faransa da Biraniya, wani mataki da ake gani a matsayin maida martani kan haramta sayen mai daga kasar Iran da Kungiyar Tarayyar Turai da yi da bai fara aiki ba tukuna.
Ma’aikatar albarkatun mai ta kasar Iran ta bayyana yau Lahadi cewa, an daina duk wata huldar cinikin mai da kamfanonin Faransa da na Biraniya kuma Tehran ta dauki matakan sayar da danyen manta da wadansu sababbin abokan ciniki.
Bisa ga dukan alamu Iran ta dauki wannan matakin ne da nufin shan gaban Kungiyar Tarayyar Turai a shawarar da ta dauka na haramta sayen danyen man kasar Iran daga ranar daya ga watan Yuli. Wannan na daga cikin yunkurin kasashen yammaci na gurguntar da samar da kudin gudanar da ayyukan nukiliyan Iran da ake takaddama a kai, da kasashen yammaci ke cewa kasar tana kokarin kera makaman nukiliya, zargin da Iran ta musanta.
Yau Lahadi ne kuma ake kyautata zaton mai ba shugaban kasar Amurka shawarwari kan harkokin tsaro Tom Donnilan zai gana da Firai Ministankasar Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Kudus yayinda ake bayyana damuwa dangane da ayyukan Iran na nukiliya da kuma rahotannin da ke nuni da cewa, yana yiwuwa Isra'ika ta kaiwa Iran harin soja.
Donilan shine jami'in Amurka na baya bayannan da zai tattauna batun Iran da Isra'ila a jerin jami'an kasar da suka tattauna a kan wannan batun.