Amurka da kuma kasashen Turai sun yi taka tsantsan yayinda suke bayyana yiwuwar samun ci gaba a tayin da Iran tayi na komawa teburin tattaunawa da manyan kasashen duniya dangane da ayyukanta na nukiliya.
Da take magana jiya Jumma’a a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Sakatariyar ma’aikatar Hillary Clinton da babbar jami’ar harkokin kasashen ketare ta Kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton sun ce suna nazarin wasikar da Iran ta rubuta inda ta bayyana niyarta ta komawa teburin tattaunawar. Wasikar da jami’in shiga tsakani na kasar Iran kan ayyukan nukiliya Saeed Jalili martani ne kan wasikar da Ashton ta aikawa Iran a watan Oktoba.
Clinton ta bayyana amsar da Iran ta bayar a matsayin wani mataki mai muhimmanci.
Kasashen biyar da kuma daya da ake kira P5+1 sun hada da membobin kwamitin sulhu biyar masu kujerar din din din, Amurka da Birtaniya da China da Faransa da kuma Rasha, daya kasar kuma da ke cikin tattaunawar ita ce Jamus.
Ashton wadda ta wakilci kungiyar wajen tuntubar Iran ta bayyana jiya Jumma’a cewa, alamun baya bayan nan sun nuna a shirye Iran take ta fara tattaunawa.
Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun kara takunkuman kan Iran sabili da fargaban da suke yi cewa tana kokarin kera makaman nukiliya. Iran dai ta nace cewa, aikinta na zaman lafiya ne.
Ashton ta bayyana cewa, takunkuman da aka kakabawa Iran suna aiki, sai dai tace al’ummar kasa da kasa sun gwammace warware batun nukiliyan ta hanyar tattaunawa.