Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius yace Iran da giggan kasashen duniya guda shidda sun cimma matakin farko na yarjejeniyar kayade shirin nukiliyar Iran, ita kuma za'a sausauta takunkunmi da aka aza mata.
Da sanyin safiyar yau Lahadin Mr Fabius ya bada wannan sanarwa a birnin Geneva a rana ta biyar na yin shawarwari.
Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif da mai magana da yawun kungiyar kasashen turai Micheal Mann, dukkansu su sa bayanai a dandalin twitter su, suna masu fadin cewa, an cimma yarjejeniya a matakin farko.
Jiya Asabar sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya iske takwarorin aikinsa daga Rasha da Britaniya da Faransa da China da kuma Jamus a birnin Geneva domin ci gaba da yunkurin ganin Ian ta kayade shirin karawa ma'adinin uranium daraja. John Kerry ya gana a kebe a gefen taron da Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov.
Shi kuma Ministan harkokin wajen Sweden ya tattauna da Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif a gefen taron a jiya Asabar