Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Foure Gnassingbe Ya Lashe Zaben Kasar Togo


Faure Gnassingbe
Faure Gnassingbe

Hukumar zaben kasar Togo ta bayyana shugaban kasar Foure Gnassingbe a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar ranar asabar.

Sakamakon zaben kasar Togo ya nuna cewa shugaban kasar mai ci yanzu Foure Gnassingbe ne ya sami nasara akan abokin karawarsa Jean Pierre Fabre, wanda hakan zai ba wa danginsa damar ci gaba da mulkar kasar na fiye da rabin karbi.

Shugaban hukumar zaben kasar Taffa Tabiou, yace Shugaban ya samu kuri’u miliyan daya da dubu dari biyu, wato kashi 59 daga cikin dari na kuri’un da aka kada. Shi kuma abokin adawarsa Jean Pierre Fabre ya zo na biyu da kashi 35 na kuri’un zaben.

Ya dai karbi mulki ne a shekarar 2005 bayan da mahaifinsa Gnassingbe Eyadema ya rasu, wanda ya mulki kasar tun daga lokacin mulkin Faransawa na tsawon shekaru 38.

Mista Fabre dai na ikrarin cewa an tafka magudi a zaben, sai dai Babban Janar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya yabawa zaben na ranar asabar, ya kuma yi kira ga shugabannin siyasar kasar da su tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG